Ta’addanci: Kotu ta yanke wa Simon Ekpa hukuncin daurin shekaru 6 a gidan yari
Kotu ta yanke wa Simon Ekpa mai fafutukar kafa kasar Biafra hukuncin daurin shekaru 6 a gidan yari

Kotun gundumar Päijät-Häme da ke kasar Finland ta yankewa Simon Ekpa, mai fafutukar kafa kasar Biafra hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa samunsa da laifin ta’addanci.
A hukuncin da ta yanke a ranar Litinin, kotun ta samu Ekpa da laifin tada zaune tsaye da kuma shiga ayyukan kungiyar ta’addanci.
A cewar Yle, wata jaridar kasar Finland, kotun ta ce Ekpa ya yi amfani da “gagarumin kafofin sada zumunta na zamani” wajen tada zaune tsaye a yankin kudu maso gabashin Najeriya tsakanin watan Agusta 2021 zuwa Nuwamba 2024.
Kotun ta kuma lura da cewa Ekpa ya baiwa wasu kungiyoyi makamai, bama-bamai, da alburusai “ta hannun mutanensa a yankin, kuma an same shi da karfafawa mabiyansa a dandalin sada zumunta na X su rika aikata laifuka a Najeriya”.
Kotun ta kuma samu Ekpa da laifin zamban haraji da kuma saba wa tanadin dokar lauyoyi.
Ekpa dai almajirin Nnamdi Kanu ne, shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB).
Bayan da aka tasa keyar Kanu zuwa Najeriya daga kasar Kenya a watan Yunin 2021, an nada Ekpa a matsayin jagoran yada labarai na Rediyon Biafra.
Makonni bayan haka, IPOB ta sanar da korar Ekpa, saboda kin sanya hannu a dokar da ta kafa gidan Rediyon Biafra. Wannan batu ya dagula alaka tsakanin IPOB da Ekpa, inda ya kafa kungiyarsa ta ‘yan aware.
Dan awaren ya yi amfani da kafafen sada zumunta na zamani musamman X wajen bayar da umarnin zama a gida a yankin kudu maso gabashin kasar, yayin da yake kira da a kai wa jami’an tsaro hari.
A lokuta da dama, IPOB ta nisanta kanta daga ayyuka da umarnin Ekpa.
A cikin Nuwamba 2024, jami’an tsaro sun kama Ekpa a Finland.
Daga baya kotu ta tura shi kurkuku saboda “yada farfagandar ‘yan ta’adda a shafukan sada zumunta”.
A cikin Maris 2025, gwamnatin tarayya ta nada Ekpa a matsayin “mai ba da kudin ta’addanci”.