Rikicin manoma da makiyaya ya barke a jihar Neja
Rikicin manoma da makiyaya ya jikkata da dama a garin Lapai

Daga Adamu Aliyu Ngulde
Rundunar yan sandan jihar Neja ta tabbatar da mutuwar mutum daya tare da jikkata wasu da dama yayin rikicin manoma da kuma Fulani makiyaya a kauyen Fako, na karamar hukumar Lapai da ke jihar Neja.
Majiyar jami’an tsaro ta shaidawa Jarida Radio cewa lamarin ya faruwa a ranar 8 ga watan Afrilu da misalin karfe 10 na dare. Inda wani mutum mai suna Usman Misa na Gidan Mangori, ya bada labarin cewa ýaýansa Habibu Usman da Abbas Usman suna kan hanyar dawowa gida daga kiwo sai wasu ýan banga matasan Fulani suka afka musu.
A cewar majiyar ýan sandan, sakamakon rashin tsayawar da masu kiwon suka yi shi ne ýan bangan suka harbe su, nan ta ke Abbas Usman ya gamu da ajalinsa, sannan daya daga cikin shugabannin ýan bangan da ke sansanin Gulu Kandi mai suna Laulo ya samu rauni.
Hakazalika majiyar tsaron tace baturen ýan sandan Lapai ya aika da jami’ansa domin kai ďauki.