“Talauci ya shiga ko’ina a fadin kasar nan” – Kwankwaso
Kwankwaso yayi magana kan tsare-tsaren 2027

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano kuma jigo a jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya nuna damuwarsa kan karuwar kunci da talauci a Najeriya.
Sanata Kwankwaso a wani rubutu da ya wallafa a shafin X ya ce jam’iyyar NNPP da shugabanninta da mambobinta ba su gamsu da halin da ake ciki a yanzu ba da kuma tarin kalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta a fadin kasar nan.
Sanata Rabiu Kwankwaso ya wallafa wannan rubutu ne sa’o’i kadan bayan da jam’iyyarsa ta gudanar da taron Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) a Abuja.
A cewar Sanata Kwankwaso, ya yi amfani da wannan damar wajen nuna jin dadinsa ga ‘ya’yan jam’iyyar NNPP bisa kokarinsu na ciyar da jam’iyyar gaba.
Ya kuma taya kwamitin murnar nasarar da aka samu a zaben jam’iyyar da aka gudanar.
Dangane da yuwuwar daidaita harkokin siyasa da kuma sake fasalin kasa gabanin zabukan shekarar 2027, tsohon gwamnan ya ce ya gargadi ‘ya’yan jam’iyyar da su guji karkatar da hankali daga sauya sheka da tattaunawa tsakanin sauran ‘yan siyasa.
“Mun gamsu da jam’iyyar NNPP, kuma mun yi imanin cewa muna da abin da za mu iya bayarwa a matakin mafi girma na shugabancin kasar nan.
Ya kara da cewa “A shirye muke mu tattauna da kowa, amma duk wata tattaunawa za ta kasance a jam’iyyance.”