Duniya

Zelenskyy ya amince da shawarar Putin na dawo wa tattaunawa a Istanbul

Zelenskyy ya amince da shawarar Putin na dawo wa tattaunawar tsagaita wuta a Istanbul

Daga Fadeelah Idris Abudulmalik

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya ce shi da kansa zai jira shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a kasar Turkiyya ranar Alhamis, yayin da kokarin diflomasiyya ke nuna alamun farfadowa bayan shafe watanni ana gwabzawa tsakanin kasashen biyu.

“Muna jiran cikakkiyar tsagaita bude wuta mai ɗorewa, daga gobe, don samar da tushen da ya dace don diflomasiyya,” in ji Zelenskyy a kan X ranar Lahadi.

“Babu ma’ana a tsawaita kashe-kashen. Kuma zan jira Putin a Turkiyya ranar Alhamis. Da kaina. Ina fatan a wannan karon Rashawa ba za su nemi uzuri ba.”

Kalaman nasa sun zo ne jim kadan bayan Putin ya sanar da cewa, Rasha a shirye take ta dawo tattaunawa kai tsaye da Ukraine a Istanbul daga ranar 15 ga watan Mayu.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button