Nijeriya

Donald Trump ya karbi takardar koke kan ci gaba da tsare Nnamdi Kanu

Trump ya karbi takardar koke kan ci gaba da tsare Nnamdi Kanu

Shugaban Amurka Donald Trump ya karbi takardar koke kan ci gaba da tsare shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPoB), Mazi Nnamdi Kanu.

An gabatar da takardar koken mai kwanan wata 28 ga Agusta, 2025 daga kungiyoyin da ke goyon bayan Igbo a kasashen waje, ta hannun lauyan Nnamdi Kanu na kasa da kasa Bruce Fein, a madadin kungiyar American Veterans of Igbo Descent (AVID), Rising Sun Charities Organisation, da kuma jakadu masu rajin kafa kasar Biafra.

Takardar ta bukaci shugaba Trump da ya kakabawa wasu alkalan Najeriya biyar takunkumi da kuma wani tsohon babban lauya a gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, bisa zarginsu da hannu a cikin halin da Nnamdi Kanu ya shiga.

Masu shigar da kara sun zargi jami’an gwamnatin Najeriya da hannu wajen keta dokokin kasa da kasa, da suka hada da sace Kanu da ake zarginsa da aikatawa, tare da tsare shi na ban mamaki da kuma gurfanar da shi gaban kotu.

Kungiyoyin sun kara da cewa jami’an shari’ar Najeriya da abin ya shafa sun ci zarafin yarjejeniyar tarurrukan kasa da kasa. Sun ba da misali da yadda Amurka ta kakabawa alkalan kasashen waje takunkumi, ciki har da Olesya Fedoseeva na Rasha, a watan Disamba 2024 kan tsare dan majalisar birnin Moscow Alexi Gorniov.

 

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button