Nijeriya

Zamfara: Sojojin Nijeriya Sun Kashe Manyan ‘Yan Ta’adda Biyar

Sojojin Nijeriya Sun Kashe Manyan 'Yan Ta'adda Biyar a Jihar Zamfara

Fadeelah Abdulmalik

Da sanyin safiyar ranar 1 ga watan Mayun 2025, dakarun Combat Team 6 na rundunar sojin Nijeriya, a yayin da suke sintiri sun yi artabu da wasu gungun ‘yan ta’adda dauke da muggan makamai bayan sun kai hari kauyen Mai Kwanugga a karamar hukumar Talata Mafara.

‘Yan ta’addan da ke tayar da tarzoma ta hanyar kai wa fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba tare da kore kauyuka, sun sha kashi a wannan karon bayan kazamin musayar wuta da sojojin Nijeriya.

Wannan arangamar dai ta yi sanadin fatattakar ‘yan tada kayar bayan da suka hada da wasu manyan ‘yan bindiga biyar masu suna Auta Jijji, Dankali, Sagidi, Kachallah Rijaji, da Kachallah Suza.

Jarida Radio

Barka da zuwa shafin Jarida Radio - Kafa Mai Inganci, domin samun labarai da dumi-dumi da zurfafa nazari da shirye-shiryen rediyo masu kayatarwa. Jarida Radio ba kawai dandalin labarai ba ne - murya ce ga al'umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button